A cikin wannan littafi mai suna Marainiya an yi amfani da wasu namun daji da kwari da iskoki. Littafin kuma tatsuniyoyi goma ne, kowace da irin abin da take koyarwa.
Daya daga cikin wadannan tatsuniyoyi ta kunshi labarin Kura ne da aka sani da hadama da zalama. Ta yi kawance da Kurege wanda aka sani da wayo da dabara. A wajen yawon neman abincin ne Kura ta so ta yaudari Kurege amma ba ta yi nasara ba.
A karshe dai Kurege ya nuna biyayya gare ta shi ne ya yi nasara, ita kuma ta sha wuya. Masu magana sun ce: Kwadayi mabudin wahala.